Ọpọlọ Lab wani kamfani ne na ƙasa da ƙasa da wasu masu rajin kishin ci gaban nahiyar Afurka suka kafa shi, saboda imanin da suka yi cewa nahiyar ita ce tushen bil Adama kuma matattarar ci gaban duniya a nan gaba. Ọpọlọ Lab na gabatar da ayyuka daban-daban: rubutacciyar fassara, fassarar kalamai kai tsaye a lokacin taruka, rubuta kalaman da aka furta, fassarar kalaman finafinai ko majigi, harkokin kasuwanci a dandalin intanet, gina shafukan intanet na kwamfuta da na wayoyin salula, samar da horon sanin makamar aiki da sauransu.
Ọpọlọ Lab na gudanar da ayyukansa a cikin muhimman yarukan duniya, yayinda a gefe ɗaya yake bada muhimmanci ga yarukan nahiyar Afurka domin taimaka wa nahiyar Afurka ta amfana da ci gaban da aka samu na ilimi. Abu ne mai muhimmanci ga masu ilimi da hikima na nahiyar Afurka da ba su iya magana da wasu yaruka na ƙasashen waje ba, da su iya samun damar yaɗa ilimi da ƙwarewar su ga sauran al’ummar duniya sannan a ɗaya ɓangare su amfana da ilimin da wasu al’ummomin da ke magana da wasu yarukan ke yaɗawa. Saboda haka, Ọpọlọ Lab ya jajirce wajen samar da ingantacciyar fassara daga yaruka na ƙetare zuwa yarukan nahiyar Afurka da kuma akasin hakan, haɗi da kuma aikace-aikacen da ya saba gudanarwa cikin yarukan nahiyar Turai da Asiya. Mun zama cibiya sha kundum da ake tunkara don samun fassara yarukan nahiyar Afurka, inda muka karaɗe fiye da yaruka ashirin na nahiyar Afurka.
Ọpọlọ Lab na aiki da ƙwararrun maaikata da kuma masu bada shawarwari da ke da hazaƙa da himma, kuma ba sa nuna bambancin ƙabila ko addini ko jinsi, ko kuma ƙasa.
Ga duk wata buƙata, a tuntuɓe mu yanzu.

SEO

á»ÂŒpá»Âlá»Â Lab® Kwaddebuwa (Cote d’Ivoire)

Remblai, Koumassi lot 2323 ilot 56, á»ÂŒpá»Âlá»Â Lab, Abidjan

á»ÂŒpá»Âlá»Â Lab® Saudiya

Bagdaddiyyah Shargiyyah

á»ÂŒpá»Âlá»Â Lab® Benin

C/2030 maison Sacca Vèdoko, Kwatano (Cotonou), Jamhuriyar Benin

á»ÂŒpá»Âlá»Â Lab® Nigeria

17, Ogbomoso Street, Area 8, Garki II, Abuja